Harin dai na wannan safiyar a cewar Kungiyar ta OSDH ya yi sanadin mutuwar mutane 58.
galibin wadanda harin ya ritsa dasu fararen hula ne da suka hada da yara 11.
Kungiyar ta ce galibin mutanen sun mutu ne sanadin shakar wani iskar gas mai guba, saidai kawo yanzu bata kai ga bayyana irin nau'in gas din ba.
rahoton ya ce da akwai fararen hula da dama da yanzu haka suke fama da matsalar numfashi.